玻璃心是什么意思
![]() | |
---|---|
![]() | |
Bayanai | |
?aramin ?angare na |
landmass (en) ![]() ![]() |
Bangare na |
Earth's crust (en) ![]() |
?asantuwa a yanayin ?asa |
continental crust (en) ![]() |
Described at URL (en) ![]() | whosonfirst.org… da wikispooks.com… |
NCI Thesaurus ID (en) ![]() | C76349 |
Hannun riga da |
ocean (en) ![]() |

Nahiya na nufin manya-manyan da'irar shimfi?a??un ?asashe da ake da su a duniya. Akan ?ididdige su ne dangane da yarjejeniya ba wai don wasu ?a'idoji na musamman ba, akwai yankuna na ?asa guda bakwai wanda ake ?auka a matsayin nahiyoyin duniya. Wanda aka jera su daga mafi girmansu zuwa mafi ?an?antansu, wa?annan nahiyoyi bakwai sune: Asiya, Afirka, Amurka ta Arewa, Amurka ta Kudu, Antatika, Turai, Ostiraliya.[1] Wasu 'yan bambance-bambance na iya ha?e wadannan nahiyoyi misali, Amurka, Eurasia, ko kuma Afro-Eurasia akan dauke su a wasu lokutan a matsayin nahiya ?aya wadanda ka iya rage yawan nahiyoyin zuwa guda hu?u.
Amma abin da aka fi ha??a?ewa akai shi ne, wa?annan nahiyoyi guda Bakwai ne. Kuma sun ha?ar da Afirka da Antatika da Asiya da Ostraliya da Turai da kudancin Amirka da kuma Arewacin Amirka. Wannan a yadda aka karantar da ?alibai kenan a yankin nahiyar Amirka baki ?aya. Ana daukan Zealandia, wani katafaren yanki na duniya a matsayin nahiya mai zaman kanta.
Amma kuma a yankin nahiyar Turai da kuma sauran sassan duniya, mafi yawan ?aliban yankunan ana karantar da su cewar, nahiyoyi Shida rak ake da su a duniyar nan. Ma'ana a wa?annan yankuna ana duban Kudancin Amirka da kuma Arewacin Amirka a matsayin nahiya guda ?aya ta Amirka. Anan lissafin nahiyoyi shidan kenan ya ha?ar da Afirka da Amirka da Antarctica da Asiya da Australiya da kuma Turai.
To sai dai a halin da ake ciki kuma, mafiya yawan masana ta fuskar kimiyya na duban wa?annan nahiyoyi Shida da cewar nahiyar Turai da ta Asiya a dun?ule suke wuri ?aya a matsayin nahiya guda, don haka ne ma suke kiran nahiyar da suna Eurasiya, sai kuma Afirka da Antarctica da Austaraliya da Kudancin Amirka da kuma Arewacin Amirka.
Masana ilimin taswirar duniya, su kuma a halin yanzu sun kasafta duniyar nan zuwa yankuna takwas domin samun sau?in fahimta. Yanki na farko dai shi ne na Asiya, wanda ya ?unshi Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka. Sai kuma Turai da Arewacin Amirka. Akwai kuma Tsakiyar Amirka da yankin Carribbean, kana kuma Kudancin Amirka da Afirka da Austaraliya da kuma Yankin Teku, wato Oceania kenan.
Yawan jama'a
[gyara sashe | gyara masomin]
Continents of the world[2] | |||
---|---|---|---|
Nahiya | Fa?in ?asa | Jumullar Mutane | |
km2 | mi2 | ||
Asiya | 44,579,000 | 17,212,000 | 4,298,723,000 |
Afrika | 30,221,532 | 11,668,599 | 1,110,635,000 |
Amurka ta Arewa | 24,709,000 | 9,540,000 | 565,265,000 |
Amurka ta Kudu | 17,840,000 | 6,890,000 | 406,740,000 |
Antatika | 14,000,000 | 5,400,000 | 4,490 (Estimated) |
Turai | 10,180,000 | 3,930,000 | 742,452,000 |
Osheniya | 8,525,989 | 3,291,903 | 38,304,000 |
Duniya | Around 7.7 billion
(As of 2019) |
Nahiya mafi yawan mutane itace Asiya, sai Afrika mai biye mata baya. Ta uku itace Turai. Ta hu?u itace Amurka ta Arewa sai ta biyar kuma Amurka ta Kudu.[3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Most people recognize seven continents—Asia, Africa, North America, South America, Antarctica, Europe, and Australia, from largest to smallest—although sometimes Asia and Europe are considered a single continent, Eurasia."
- ↑ "Map And Details Of All 7 Continents". worldatlas.com. Retrieved 6 March 2016.
- ↑ "These maps show where the world's youngest and oldest people live". Public Radio International.